ECOWAS ta soke zuwa sasanci a Gambia

ECOWAS ta soke zuwa sasanci a Gambia

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun soke kai ziyara a wannan Laraba a kasar Gambia a kokarin shawon kan Yahya Jammeh don ganin ya mika ragamar mulki ga Adama Barrow, in da aka dage kai ziyarar har zuwa ranar juma’a mai zuwa.

ECOWAS ta soke zuwa sasanci a Gambia

ECOWAS ta soke zuwa sasanci a Gambia

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, duk da cewa an dage ganawar da aka tsara yi a yau laraba, amma fa matsayin shugabannin kasashen yankin na ganin cewa Jammeh ya mika ragamar mulki a karshen wa’adinsa na nan daram.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin gwamnan jihar Delta na rokon yan bindiga su daina kai hare-hare

Wannan kuma na zuwa ne a wani lokaci da babban mai sharia na kasar Emmanuel Fagbenla ya sanar cewa, a cikin watan biyar ko na sha-daya za su saurari batun makudi da Yahya Jammeh ya ce an yi a zaben.

A farko dai shugaba Jammeh da ya mulki Gambia na tsawon shekaru 22 ya amince da shan kayi a zaben na watan jiya, amma daga bisani ya tubure bayan ya zargi jami'an hukumar zaben kasar da tafka kura-kurai.

Ku biyo mu a Facebook: https://web.facebook.com/naijcomhausa/

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel