Sanata Orji yace kasada ne sanata ya dinga fada da gwamnan jihar sa

Sanata Orji yace kasada ne sanata ya dinga fada da gwamnan jihar sa

Tsohon gwamnan jihar Abia, kuma sanata mai ci a yanzu dake wakiltar mazabar Abia ta tsakiya, Sanata Theodore Orji yace bai kamata sanata ya dinga fada da gwamnansa ba, kasada ne.

Sanata Orji yace kasada ne sanata ya dinga fada da gwamnan jihar sa

Sanata Orji

Sanata Orji ya bayyana haka ne yayin dayake tsatstsage ma al’ummar mazabansa bayanin aikace aikacen da yayi a matsayinsa na wakilinsu a garin Umuahia na jihar Abia, inji rahoton jaridar Authority.

KU KARANTA:Gawa ta ki rami: Akwatin gawa ta karye, gawa ya faɗo

Gwamnan yace bata lokaci ne kawai Sanata ya dinga fada da gwamnan jiharsa, saboda gwamnan yafi karfinsa sakamakon karfin iko da tsarin mulki ya baiwa gwamna. Don haka ne sanatan ya gargadi masu nufin kulla rikici tsakanin gwamna Okezie Ikpeau da sauran masu rike da mukamai da su dai na.

Orji yace: “Babu yadda zaka yi nasara idan ka fara fada da gwamna, saboda yana da karfin ikon da baka da shi, don haka ya kamata mu baiwa gwamnan mu goyon baya, ba wai mu kwance mai zani a kasuwa ba.''

Dandane da rikicin jam’iyyar PDP kuwa, Sanata Orji ya cigaba da fadin, “ina rokon ku kada ku koma wata jam’iyya, ina baku tabbacin PDP zata dawo da karfinta. Babu abinda wata jam’iyya zata iya baku.”

A wani labarin kuma, Sanata Theodre Orji ya bukaci a kafa wata cibiyar kwararrun yan siyasa, Orji ya bayyana haka ne a ranar 31 ga watan Mayu na 2016 sa’ilin da ake muhawara a zaman majalisar ta dattijai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel