Sakamakon binciken AGF akan Babachir da Magu ta nuna

Sakamakon binciken AGF akan Babachir da Magu ta nuna

Sakamakon binciken wasu manyan ma’aikatan gwamnati da babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a , Abubakar Malami (SAN),keyi ta nuna, Daily Trust ta bada rahoto

Sakamakon binciken AGF akan Babachir da Magu ta nuna

Sakamakon binciken AGF akan Babachir da Magu ta nuna

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Malami ya bincike wadannan manyan ma’aitan gwamnatin wanda ya kunshi sakataren gwamnatin tarayya ), Babachir David Lawal da mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu.

Majiyoyi a ofishin ministan tace Malami yayi kokari sau 3 a karshen makon nan ya aukawa shugaba Muhammadu Buhari sakamakon binciken amma bai samu yayi ba.

KU KARANTA: APC tayi na'am da tsige Ndume

Majiyar wanda aka sakaye sunan say ace AGF yayi kokari wajen tuntuban dukkan ma’aikatun gwamnatin da aka ambata cikin tuhumar da ake yiwa Magu da Babachir.

“Anyi wannan ne domin samun Karin bayani akan abinda ke cikin takardan, a wasu lokuta AGF bai dogara ga martanin da yazo kan karar ba amma kan abinda ya samo daga hannun ma’aikatun da sunansu ya ambatu cikin martanin.”

Zaku tuna cewa a watan Disamban 2016, Shugaba Buhari ya umurci AGF ya gudanar da bincike akan tuhumar rashawan da ake yiwa wasu ma’aikatan gwamnati manya.

A jawabin da mai Magana da yawun shugaban kasa,Garba Shehu,ya gabatar,, yace duk ma’aikacin gwamnatin da aka samu da kasha a gindi cikin zargin sai ya amsa tambaya.

Duk da cewa ba'a ambaci sunan kowa ba, sakataren gwamnatin tarayya da shugaban hukumar EFCC dai an tuhume su da ayyukan rashawa.

Amma an an bada rahoton cewa shugaba Buhari da babban lauyan tarayya Abubakar Malami sun gana a ranan juma’a, 6 ga watan Junairu.

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel