Rikici ya ɓalle tsakanin ɗaliban jami’a kan kyautan N500,000 da gwamna ya basu

Rikici ya ɓalle tsakanin ɗaliban jami’a kan kyautan N500,000 da gwamna ya basu

Daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) sun dambace bayan kyautan N500,000 da da gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya basu.

Rikici ya ɓalle tsakanin ɗaliban jami’a kan kyautan N500,000 da gwamna ya basu

Jami'ar LAUTECH

Da fari dai daliban sun fito ne suna gudanar da zanga zangar nuna bacin rai game rufe makarantar tasu da mahukunta suka yi tun sama da watanni bakwai da suka gabata.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yayin da daliban ke gudanar da zanga zangar ne sai gwamnan Ajimobi ya aiko musu da sakon yana bukatar ganawa da shuwagabannin daliban don su wakilce su, tare da basu tabbacin sake bude makarantar.

KU KARANTA:Soyayya: Sabbin ma’aurata a sansanin yan gudun hijira sun samu tagomashi

Rikici ya ɓalle tsakanin ɗaliban jami’a kan kyautan N500,000 da gwamna ya basu

Gwamna Ajimobi

Bayan wakilan daliban sun kammala ganawa da gwamnan ne sai ya basu kyautan naira dubu dari biyar (N500,000) don su sha ruwa, abinka da kudi masu hada rigima, sai daliban suka fara cacar baki kan yadda ya kamata a raba kudin, kafin kace kule! Sun fara dambe tsakanin su a farfajiyar ofishin gwamnan.

Daya daga cikin shugaban daliban Fawole Israel ya bayyana ma manema labarai cewar rikicin ya faro ne lokacin da wasu shuwagabannin daliban suka yanke shawarar cewa a dibi wani kaso na kudin a watsa ma sauran daliban dake jiransu a waje.

Shi kuwa Olanrewaju Umar daya daga cikin yan majalisar dokokin kungiyar daliban Najeriya (NANS) ya ga baiken shuwagabannin daliban LAUTECH da suka amshi kyautan kudin daga hannun gwamna tun a tashin farko. Shima wani dalibin jami’ar Oyedeji Ahmed ya caccaki gwamnan daya bada kudin, inda yace:

“akan me gwamnan jihar Oyo zai baiwa dalibai kyautan makudan kudi har N500,000? Bayan har yanzu baya iya biyan albashin ma’aikatan jihar sa.”

Sai dai mashawarcin gwamna Ajimobi kan harkar dalibai da matasa Bolaji Azeez ya kare manufar gwamnan, inda yace gwamnan ya bada kyautan ne a matsayinsa na uba.

ana iya samun mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel