Hukumar Soji ta gargadi jama’a kan sabon salon kai hare hare da Boko Haram ta sauya

Hukumar Soji ta gargadi jama’a kan sabon salon kai hare hare da Boko Haram ta sauya

Hukumar Soji ta sanar da wani gargadi dangane da sabon salon kai hare hare da kungiyar Boko Haram ta kirkiro musamman a yankunan da suka fi kusa da yayan kungiyar, sa’annan ta ja kunnen jama’a da su bi a hankali da mutane masu kwankwasa musu gida.

Hukumar Soji ta gargadi jama’a kan sabon salon kai hare hare da Boko Haram ta sauya

Babban hafsan Soji Olanisakin

Mataimakin kaakakin rundunar sojan kasa kanal Mustapha Anka ne ya bayyana haka a ranar Litinin 9 ga watan Janairu, sakamakon harin da yan kungiyar Boko Haram ta kai a yan kwanakin nan.

Kanal Anka ya shaida cewar yan mata biyu ne suka kai harin kunar bakin wake a gidan wani mutumi mai suna Bulama bayan sun kwankwasa masa gida ya bude. Don haka yayi ma jama’a kashedi da su kula da irin bakin da suke yi. Ga dai yadda sanarwar take:

KU KARANTA:Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya

“Manufar fitar da wannan sanarwar shine don janyo hankalin jama’a game da sabon salon kai hari da Boko Haram suka tsira. A yan kwanakin nan wasu yan mata sun kai harin kunar bakin wake a gidajen wani Usman da Bulama duk a unguwar Kalari na garin Maiduguri.

“Yarinyar Bulama ce ta bude kofar gidansu, shi kuwa Usman, da kansa ya bude nasa kofar, nan da nan yan matan suka tashi bamabaman dake daure a jikkunansu, sanadiyyar haka suka kashe karamar yarinyar da Usman.

“Don haka ne muke gargadin jama’a dasu sanya ido sosai musamman game da irin bakin da suke samu. Mu sani, al’amarin tsaro ya shafi kowa, don haka muke rokon mutane da su kawo karar duk wani mutumi da basu yarda da shi ba ba tare da bata lokaci ba. Kuma muna kara jadda batun dokar t abaci daga karfe 10 na dare. Duk wanda aka kama yayi kuma da kan shi.”

Ana iya samun mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel