DSS da damke yan Boko Haram 13

DSS da damke yan Boko Haram 13

- Hukumar DSS tace ta damke wasu yan baranda a fadin kasa Najeriya

- DSS ta jaddada niyyanta na bada tsaro ga rayuka da dukiyan mutane masu biyyaya ga dokar kasa

DSS da damke yan Boko Haram 13

DSS da damke yan Boko Haram 13

A yunkurin ta na yaki da rashawa, hukumar tabbatar da tsaro na cikin gida tace ta samu wani gagarumin nasara akan yan baranda,masu garkuwa da mutane da yan ta’adda a fadin kasa.

Hukumar tace nasarorin da take samu ya durkusar da karfin yan barandan wajen aikata ta’asa.

Wata jawabin da Tony Opuiyo ya saki a madadin hukumar a ranan 1 ga watan Junairu,2017,a Mutum Biyu karamar hukumar Gassol jihar Taraba,an damke yan baranda masu suna Bale Kolomi Grema da Kolomi Adba-Aji a wai masallaci bayan sun gudu daga Marte jihar Borno.

KU KARANTA: Za'a cigaba da garkame lauyoyi masu rashawa

Kana an damke Amadu bello a Hotoron Arewam karamar hukumar Nasarawa,jihar Kano wanda ke cikin masu garkuwa da mutane a kauyen Zomo, karamar hukumar Ningi jihar Bauchi inda ya samu miliyan 3 na fansa.

A wata labara mai kama da haka, an damke wani gagarumin da baranda mai suna Paul ALI (aka Simplee),a ranan 6 ga watan Junairu a dakin masaukin Hill Flower Hotel, Asaga Ohafia,jihar Abia. Ya kasance mai sansuna Ikot Abasi da Mbo a jihar Akwa Ibom.

Kana kuma mamban kungiyar yan bindigan Bakassi Strike Force (BSF) wadanda suka kai hare-hare kafufuwan man fetur a yankin. A lokacin da aka kama shi, yana tare da abokin aikinsa ne Chidiebere KANU inda suke shirin yin garkuwa da wani dan majalisa.

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel