A karshe de Shugaba Buhari zai ziyarci kudu maso gabas

A karshe de Shugaba Buhari zai ziyarci kudu maso gabas

- A karshe Shugaba Buhari zai bude wasu ayyukan gwamnatin tarayya a yankin kudu maso gabashin Najeriya a wata Maris mai zuwa.

Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gama shirin ziyarar yankin kudu maso gabashin Najeriya a watan Maris, shekara 2017 a inda zai bude wasu ayyukan da gwamnati ta aiwatar.

A cewar wani rahoton ta Vanguard, ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari sai bude wasu ayyukan gwamnatin tarayya a wannan yanki. Wasu daga cikin ayyukan ne sake farfado da babban titinan mota ta Enugu-Onitsha da kuma Enugu-Port Harcourt, da sauransu.

Wata kungiyar goyon bayan Shugaba Buhari ta gafe jihar Enugu ta sanar da wannan ziyarar a wata ganawar su da sauran kwamitin kungiyar goyon bayan Buhari a yanki.

Kungiyar tace kuma ta na shirin wata liyafa ga wasu sababbin mambobin jam’iyar APC ta wannan yanki kudu maso gabas, kamar tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, Sanata Jim Nwobodo, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani, da sauransu.

Shugaban kungiyar goyon bayan Shugaba Buhari ta jihar Enugu, shugaba Anike Nwoga ta nemi babban kungiyar ta iyamurai Ndigbo ta yi imani da gwamnatin tarayya cewa kungiyar tana da tabbacin cewa a bayan lokaci kadan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zai aiwatar da duk alkawuran da ya wa yankin.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel