Makiyaya sun shiga jami’ar Ojukwu, wannan ya zama abin magana

Makiyaya sun shiga jami’ar Ojukwu, wannan ya zama abin magana

Shanaye sun zama tamkar dalibai a jami’ar Ojukwu a yankin Kudu maso gabashin kasar.

Makiyaya sun shiga jami’ar Ojukwu,wannan ya zama abin magana

Makiyaya sun shiga jami’ar Ojukwu,wannan ya zama abin magana

Fulani makiyaya sun shiga jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu University wanda aka ce ya hana dalibai karatu.

Game da cewar jaridar Vanguard, kashin shanu ya cika ko ina a cikin jami’ar kuma wasu shanayen na shiga cikin ajujuwan karatu,har wuraren da aka aiki.

Game da cewan wadanda sukayi Magana ga jaridar, shanayen sun zama tamkar daliban jami’ar saboda babu wanda ya shirya koransu.

KU KARANTA: An tsige Ali Ndume a matsayin shugaban masu rinjaye

“Abin kunya a ga irin wannan abu a jami’a kullun kuma ina mamakin abinda shugabancin makaranta keyi akan wannan abin. Wani zubin sia ka jirasu sun gama wucewa zaka iya wucewa ko kana sauri.”

Wani ma’aikacin jami’ar mai suna Douglas yace akwai lokacin daliban sukayi niyyan daukan mataki amma aka hana su. Yace wani zubin za’a garken shanu na lalata amfanin gona.

“Na san shugabannin makaranta zasu iya magance wannan abu idan sukayi niyyan yi, amma da alamun cewa suna tsoro kuma ban san me yasa ba.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel