Ma’aikatan Jihar Kwara za su samu sauki

Ma’aikatan Jihar Kwara za su samu sauki

– A Jihar Kwara, Ma’aikata za su samu sa’ida bayan da Gwamna ya bada umarni a biya wasu kudi

– Gwamnatin Jihar Kwara dai ta kwashi watanni 6 ba ta biya Ma’aikata albashin da ya dace ba

– Gwamna Abdul Fatahi ya bada umarnin sakin Naira Biliyan 2 ga Hukumar SUBEB

Ma’aikatan Jihar Kwara za su samu sauki

Ma’aikatan Jihar Kwara za su samu sauki

Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya bada umarnin sakin wasu makudan kudi domin biyan Malaman Makaranta a Jihar. Ma’aikatan Makaranta na bin Gwamnatin Jihar Kwara dai bashin albashi har na watanni 6.

A kwanan ne gwamnatin tarayya ta ba Jihar Kwara Naira Biliyan 3.77, wannan yana cikin wani kaso da Gwamnatin ke bi bashi. Tuni dai Gwamna Ahmed ya bada umarnin a biya Ma’aikatan Kananan Hukumomi da Malaman Makaranta albashi da fanshon su.

KU KARANTA: Gwamna ya yi awon gaba da kudin Bill Gates

Kwamishinan kudin na Jihar, Alhaji Demola Banu ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta aiko wannan kudi ranar Litinin. Kwamishinan yace za ayi amfani da kudin ne wajen biyan Ma’aikata kudin su.

A jiya muka kawo rahoto cewa yanzu haka a Garin Ilorin, Malaman Makaranta da dama sun koma azumi inda suke rokon Ubangiji ko a samu a biya su albashin su na wata-da-watanni. Ma’aikatan Makaranta na bin Gwamnatin Jihar Kwara dai bashin albashi har na watanni 6. Sai dai da alama Ubangiji ya karbi addu’ar su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel