Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

– Shugaban Kasa ya kori shugaban Hukumar FRC ta Kasa

– Hukumar CAN tace Shugaba Buhari yayi mata daidai

– Sakataren CAN na Kasar yace duk wanda ya shirya yaki da coci, ba zai kai ga ci ba

Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

A daren Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Mista Jim Obazee daga matsayin sa na Shugaban Hukumar FRC ta Kasa. Kuma ba tare da bata lokaci ba Shugaban Kasar ya nada Mista Adedotun Sulaiman a matsayin wanda zai maye gurbin sa.

Kungiyar CAN ta Kiristocin Katolika na Najeriya ta yabawa Shugaba Buhari da daukar wannan mataki. Sakataren CAN din Musa Asake yace duk wanda ya shirya fada da coci ba zai kai labari ba.

KU KARANTA: Gambia: Najeriya za ta kwaso Yan Kasar ta

CAN tace an yi daidai da aka kori Jim Obazee. Kungiyar tace Ubangiji ne ya daura sa, ko daga baya sai ya koma nema ya rusa coci. Sakataren na CAN yace yayi ta kokarin fadakar da tsohon Shugaban sai dai yayi mursisi.

An dai samu matsala bayan Jim Obazee ya dabbaka wata doka da ta nemi Shugabannin Addini su ajiye aiki bayan shekaru 20. Wannan dai ya kawo babban rikici musamman wajen Kiristocin Kasar har wani babban Fasto yayi ritaya. CAN dai ta shawarci Buhari da ya rabu da lamarin addini gefe guda.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel