Rikicin Kudancin Kaduna: Gwamna ya kama masu laifi

Rikicin Kudancin Kaduna: Gwamna ya kama masu laifi

– Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa ya kama masu tada rikicin Kaduna

– Gwamnan ya bayyaa sunayen wadanda aka kama da laifi

– Mal El-Rufa’i ya kai ziyara Ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar

Rikicin Kudancin Kaduna: Gwamna ya kama masu laifi

Rikicin Kudancin Kaduna: Gwamna ya kama masu laifi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta gano, ta kuma kama wadanda ke da laifi a cikin rikicin Kudancin Jihar Kaduna. Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara Ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda.

Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana sunayen wadanda aka kama lokacin da ya kai ziyara Ofishin Agyle Abeh, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna. Duk da yake Gwamnan bai bayyana sunayen masu tada rikicin a fili ba, yayi alkawarin hukunta masu laifin.

Gwamnan Jihar yace ba za su kyale a rika abin da aka ga dama ba a Jihar na rikici tsakanin Fulani Makiyaya da kuma ‘Yan Gari wanda an dade ana fama. Har dai wasu na ganin abin kamar rikicin addini

Kwanaki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a dauki kwararan matakai da suka dace wajen ganin an kawo karshen rikicin Yankin Kudancin Kaduna. Shugaba Buhari ya umarci Hukumar NEMA ta bada agajin gaggawa ta bincika irin barnar da aka yi da kuma agajin da ake bukata.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @ http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel