YANZU YANZU: An gano ma’aunin saita lokacin tashiwar bam ta Boko Haram

YANZU YANZU: An gano ma’aunin saita lokacin tashiwar bam ta Boko Haram

- Jami’in tsaro na NSCDC ta gefen jihar Borno ta gano wata ma’aunin saita lokacin tashiwar bam ta ‘yan ta’adda Boko Haram.

- An samu wannan ma’aunin ne a inda wata bam ta tashi ranar lahadi da ta gabata.

Rundunar NSCDC ta gefen jihar Borno a yau Talata, 10 ga watan Janairu, ta ce ta gano wata ma’aunin mai ƙidayar lokaci wanda ‘yan ta’adda Boko Haram ke amfani da ita a lokacin fashewar bamabamai. Babban kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Abdullahi ya yi wannan furuci ne a wata ganawa da manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar borno.

A cikin rohoton jaridan Vanguard, Abdullahi ya bayyana cewa an samu wannan na’urar ne a filin da bam ya tashi a ranar lahadi, 8 ga watan Janairu a Kalleri cikin babban birnin jihar Borno.

Mutane 8 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukan su sanadiyar bamabamai ‘yan kunar bakin wake a wurare daban daban a kalleri a ranar lahadi da ta gabata. ‘Yan kunar bakin waken ta kai hari ne ga sansanin rundunar tsaro ta farar hula JTF ta gefen garejin Muna da kuma unguwar Kalleri.

Abdullahi ya ce: “Wannan na’urar na ba ‘yan kunar bakin waken wata dama saita lokacin da suka bukaci fashewar bam. Tun da mun gano wannan na’urar jami’in tsaro za su bincike asali inda aka kerasu.”

Malam Abdullahi ya shawarci al’umma cewa a zama masu kula.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel