An hallakar da makiyaya biyu

An hallakar da makiyaya biyu

- Akalla makiyaya biyu sun hallaka a jihar Anambra

- Makiyaya biyu ne suka hallaka a wata gari Umuoba-Anam ta karama hukumar Anambra maso gabas a jihar Anambra.

Jami’ar ‘yan sanda ta tsare akalla mutane 6 game da wannan kisa, amma har yanzu ba gano wayanda suka aikatar da wannan danye aiki ba.

A yanzu jami’ar ‘yan sandan jihar Anambra na kan bincike sanadiyar mutuwar makiyayan.

Jaridan Vanguard ta rahoto cewa babban kwamishinan ‘yan sanda ta jihar Anambra Samuel Okuala yace, tuni ya tura babban adadin 'yan sanda zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana daukar fansa.

Shugaban kungiyar kiwo da suna Miyetti-Allah, Alhaji Sadiq Gidado, ya shaida wa manema labarai a Awka cewa, lamarin ya faru a yankin inda mutanen biyu da kuma wasu makiyaya ke kiwon dabbobi.

A cewar shi, an yi awon gaba da wadannan makiyayan ne a hanyar wata kasuwa mai suna Otuocha a garin Eziagulu-Otu. A yanzu ba labari game da wadannan mutane.

Gidado yace “bayan yarjejeniya tsakanin mu da gwamnatin jihar da kuma jami’ar tsaro na gani an cimma wata zaman lafiya a wannan yanki, wasu bata gari na kokarin haddasa fitina.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel