LABARI DA DUMI-DUMI: Fayose ya bude wa Buhari wuta

LABARI DA DUMI-DUMI: Fayose ya bude wa Buhari wuta

Gwamna jihar Ekiti Ayodele Fayose ya yi suka ga gwamnatin shugaba Buhari akan wata barazana da kuma kisan gilar da ake wa jama’ar kiristoci a fadin Najeriya.

Gwamna Fayose ya gargadi gwamnatin tarayya ta yi anzari maganta wannan masalolin. Ya kuma gargadi shugaba Buhari cewa, ya kula fa, kuma ya maida hankali kan wannan damuwar saboda sakamakon gazawar zai iya jawo wa kasar wata babban masifa.

Fayose ya bukaci gwamnatin tarayya ta zama mai fadar gaskiya ga al’umma a kowani lokaci. Wannan zai iya ba jama’a dama zani manufofin gwamnati.

A cewar sa, na sha yi wa wannan gwamnatin shugaba Buhari gargadi cewa su daina azabtar da kiristoci duk inda suke a Najeriya.

A ranar asabar, 7 ga watan Janairu ne Fayose ya yi wannan gargadi a inda yake tofa albarkacin bakin sa ga wata doka na gwamnatin tarayya wanda ya shafi gudanar da ayukan coci a nan kasar.

Ita wannan dokan ne sanadiyar wani babban fasto ta cocin Redeemed Christain church of God (RCCG), fasto Enoch Adeboye ya sauka daga kan gadon mulkin cocin.

Jaridan Daily Trust ta rahoto cewa, nan ba da jumawa ba wannan dokan zai tillas wa sauran fastocin, kama fasto Williams Kumuyi sauka gada karagan mulkin cocin.

Gwamna Fayose ya yi wannan bayani ne a wani shagalin bikin haihuwa cika shekara 52 na uwargidan gwamna Feyisetan Olayemi Fayose, a fadar gidan gwamnatin jihar Ekiti.

Gwamna na cewa “ana zubar da jinni kiristoci a kudanci jihar Kaduna, kuma manya manyan mutane sun gaza yin tir da wannan al’amari saboda tsoron gwamnati. Ku tuna fa, kuna a raye yanzun, wata rana sai labara. Dole ne mu hada baki mu yi tir da al’amarin.”

A wata ganawar, Fayose ya na mai mikar da ta’aziya ga iyalan sojojin da ‘yan Boko Haram ta hallaka a ranar juma’a 6, ga wata Janairu a garin Buni Yadi ta jihar Yobe.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel