Abubuwa 10 da ya kamata ka kiyaye idan kana son zama attajiri a 2017

Abubuwa 10 da ya kamata ka kiyaye idan kana son zama attajiri a 2017

Ga mai son zama attajiri yana da kyau ya guji wadannan abubuwa 10 musamman a wannan shekara ta 2017 a cewar wani kwararre kan harkar kasuwanci a wannan makala

Abubuwa 10 da ya kamata ka kiyaye idan kana son zama attajiri a 2017
Tashi da wuri na taimakawa wajen samun arziki

1. Kar ka taba tashi da wuri

Ka yi ta bacci a kan gadoka har sai kaji yunwa ta yanda ba za ka iya cigaba da bacci ba. Kai da ba kudin cizo akan gadonka danme zaka tashi da wuri?

2. Karka taba tsara yanda zaka kashe kudin ka

Duk lokacin da kasamu kudi kawai ka bi ta kan su idan suka kare sai ka tsaya ka tuna nawa ka kashe kuma ta yaya ka kashe su.

3. Karka taba tunanin tattali har sai ka samu makudan kudade

Sabo da me za ka yi tattali kai da kake samun kudi kadan? Masu cewa ka yi tattali ba sa tausawa bukatunka ne.

4. Yi ta harbata mati kawai

Ba ruwan ka da tsare-tsaren da a ka yi da wadanda ba su yi karatu mai zurfi ba. Tayaya ma kai da ka yi Digiri za ka yi wani karamin kasuwanci? Irin wannan ai sai wadanda ba su je makaranta ba.

5. Kar ka yi tunanin fara sana'a har sai an aiko maka da jari daga sama

Me zai sa ayi tsammanin ka fara zuba jari kafin ka samu miliyoyin Naira? Duk da cewa, fiye da rabin kasuwanci a garinku yana bukatar "yan daruruwa ne don farawa, kai da kake Babban Yaro ba zaka fara ba sai ka samu miliyoyi.

6. Ka yi ta korafi a kan komai ban da halayenka

Ka yi ta zargin tsare-tsaren gwamnati da na bankuna da suka hana samun bashi. Dukkan su mutanen banza ne da basu so kayi kudi.

7. Ka dinga kashe fiye da abin da kake samu

Dan cimma hakan ka yi ta karbar kaya bashi tare da rantar kudaden abokai da wadanda kakewa aiki.

8. Ka yi ta gasar sanya kaya

Ka tabbata cewa kai ne ka ke sa sabbin kaya na kece raini a tsakanin ma'aikatan ofis dinku. Idan kaga abokin aikin ka ya sayi sabuwar wayar hannu, ka yi kokari ka sayi wacce tafi tasa tsada.

9. Ka sayi mota tsaleliya

Dan dan kudin da ka samu, yi kokari sayi mota wacce ta zarce rubi-uku na abinda kake samu a wata.

10. Ka baiwa 'ya 'yankan duk abin da suke bukata

Tunda kai uba ne mai kaunar 'ya 'yansa. Kar su koyi kowace irin sana'a saboda ba ka so su sha wahala. Za su tashi malalata ta yanda ba za su iya taimaka maka ba lokacin da girma ya zoma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel