Jami’ar ABU Zaria ta yaye dalibai 11,000

Jami’ar ABU Zaria ta yaye dalibai 11,000

- Jami’ar ABU Zaria ta yaye dalibai sama da 11,000 a karshen wannan makon

- Jami’ar ta yaye dalibai masu digiri da digirgir har ma da digir-digir

- Ciki an samu guda 49 da suka ciri tuta

Jami’ar ABU Zaria ta yaye dalibai 11,000

 

 

 

 

 

 

 

 

Jami’ar Ahmadu Bello watau ABU Zaria ta yaye dalibai a karshen wannan makon. Jami’ar da it ace ta farko a Arewacin Najeriya ta yaye dalibai masu digiri guda 11, 731. Kamar yadda muka samu labari akwai guda 2, 697 masu shaidar Digiri na biyu, sannan kuma guda 289 sun kammala karatun Digiri na uku.

Shugaba Buhari ya ce za ayi bincike game da irin badakalar da ake samu a cikin Jami’o’i. Shugaban Kasar yayi kira da Jami’ar ta ABU Zaria da ta maida hankali wajen nazari game da harkar noma. Farfesa Rasheed na Hukumar NUC ne ya wakilci Shugaban Kasar.

KU KARANTA: An karamma Shugaban Hukumar NUC, Farfesa Rasheed

Shugaban Jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana irin cigaban da Jami’ar ta samu wajen fanni dabam-dabam a karkashin Shugabancin sa. Farfesa Garba ya kira daliban da aka yaye su zama masu tarbiya bayan ilmin da suka samu.

Cikin daliban da aka yaye akwai guda 49 da suka samu gamawa da shaidar mataki na farko watau digiri first class. Kwanan nan ABU Zaria ta kera matatar man fetur, sannan kuma ta gano wani maganin cutar malaria na ciwon sauro.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel