Keke NAPEP mai amfani da hasken rana (Hotuna)

Keke NAPEP mai amfani da hasken rana (Hotuna)

Wani matashi ya taya abokinsa mai suna Ekomobong Finbarr murnar kera wata mashin din Keke NAPEP mai amfani da hasken rana a jami’ar kimiyya ta Owerri.

Dan uwan Ekomobong ya daura hotunan abokin nasa da dama yayin da yake tuka malamansa cikin mashin din daya kera da hannunsa.

Keke NAPEP mai amfani da hasken rana (Hotuna)

Yayi ma wasu hotunan taken “ina alfahari da kanina Ekomobong Finbarr. A satuttukan da suka gabata ne dai ya kammala kera mashin din Keke NAPEP mai amfani da hasken rana, wannan jirgi daya kera na cikin sharuddan kammala karatunsa na digiri daga tsaganyar kimiyyar lantarki na jami’ar kimiyya dake Owerri. Mashin din bashi da inji, batir kawai ake sa mai, sai hasken rana, a haka sai da yayi tafiyan kilomita 11.”

KU KARANTA: Duba abin mamakin da aka gani a Abuja (Hotuna)

Su kansu malaman Ekomobong Finbarr sun cika da mamaki yadda ya iya hada wannan mashin. Shugaban tsangayar tasu Mista Damian Dike da wata malama Achumba sun shiga mashin din, kuma yaron ya tuka su.

Ga su daga cikin hotunan:

Keke NAPEP mai amfani da hasken rana (Hotuna)
Keke NAPEP mai amfani da hasken rana (Hotuna)

&index=148&list=PL6sEiOi0w1ZCmg6rIvhdW7Xeicx_0Gk05

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel