Yawan kudin fanshon da tsohon Ambasada ke karba

Yawan kudin fanshon da tsohon Ambasada ke karba

Tsohon jakadan Nijeriya a kasar Masar da Iran, Ambasada Umar Bashi Wali, a jiya Litinin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dube shi kan naira dubu biyu da dari hudu da yake karba duk wata a matsayin kudin fanshon sa.

Yawan kudin fanshon da tsohon Ambasada ke karba
Tsohon jakadan Nijeriya a kasar Masar da Iran, Ambasada Umar Bashi Wali

A yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust, Ambasada Wali ya kara da cewa ya dauki tsawon shekaru wajen yi wa kasa hidima, inda a shekarun baya ake biyansa naira dubu hamsin a matsayin fanshon nasa a duk wata.

Ya kara da cewa duk gyaran da aka yi a fannin kudin fansho kudin da ake biyansa yana nan a yadda yake maimakon a kara masa.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da karatun difloma a jami'oin Najeriya

"Duk da cewa a matsayina na tsohon Ambasada wanda ya yi wa kasa aiki a tsawon shekaru 36, na kai tsawon shekaru takwas ina karbar naira 1,800 a duk wata a matsayin kudin fanshon nawa, daga baya aka kara zuwa 2,400.

"Yanzu na kai shekaru 82 kuma na tsufa. Na rubuta korafi da dama kan hakan zuwa ofishin kula da kudin fansho dake Abuja amma babu amsa. Kuma na je har ofishin da kaina domin mika korafi na kan lamarin. Inda suka yi alkawarin gyarawa amma har yanzu shiru. Don haka ina kira ga wadanda ke da alhaki kan lamarin da su taya ni yin duba kan lamarin", inji Ambasada Bashir Wali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel